Call for Nomination for She Stands for Peace ebook - Hausa

16 Sep 2021

Call for Nomination for She Stands for Peace ebook - Hausa

Ana gayyatar jama’a da su ba da sunayen Matan Afirka wadanda sukayi fice wajen cigaban Mata, Zaman lafiya da Ajandar Tsaro a Afirka “TA JAJIRCE WAJEN SAMUN ZAMAN LAFIYA” Littafin yanar gizo (Ebook).

QARIN BAYANI

A watan fabrerun shekarar 2020, Ofishin Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin kan Ofishin Hada kan Afirka ya wallafa littafin tunawa da bikin cikar shekaru ashirin da kafuwar UNSCR 1325 a shekarar (2000). Sunan littafin shine; ‘Ta Jajirce domin Zaman Lafiya: shekaru ashirin Balaguro ashirin’.

Littafi ya karrama muhimman gudumawar da mata suka ba da wajen samar da zaman lafiya idan aka yi la’akari da tashe-tashen hankula da suka addabi nayiyar Afirka a wannan lokacin. Shawarar amincewa da rubuta labarin gwagwarmayar da wasu mata su goma sha shida suka yi da kuma wasu kungiyoyin mata su hada wannan shawarar ta samu amincewar jama’a da dama a dukkannin sassan nahiyar har ma shugabannin mata da kuma kungiyoyin mata.

Sauraron muryar mace da gudumawar ta ya zama dole a matsayin zakaran-gwajin-dafi wajen irin rawar da mata za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

A wannan matsayi ne za a samu hadin guiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Hada kan Afirka (UNOAU). A wallafa “Ta Jajirce Domin Zaman Lafiya” (Littafin Yanar gizo).

wasu daga cikin muhimmancin littafin sun hada da:

 • Amincewa da gudumawar da mata da kuma kungiyoyin mata suka bayar domin tabbatar da zaman lafiya a daukacin Nahiyar Afirka baki daya.
 • Wallafa tarihin rayuwar mata a wasu wuraren tare da bayyana gwagwarmayar da mata suka yi domin samar da zaman lafiya mai dorewa a matakai daban-daban.
 • Gabatar da dabaru kai-tsaye domin aiwatar da Kudirin Majalisar Dinkin Duniya (unscr 1325) daga shekarar 2020 dangane da tarihin rayuwar su domin gina tabbataccen zaman lafiya mai dorewa da aiwatar da kudirin (WPS) a Afirka.
 • Zabarar da masu ruwa da tsaki wajen samar da yanayin da ya dace domin bai wa mata gudumawa domin su taka rawa ta musamman wajen gina ingantaccen zaman lafiya kamar yadda Kudirin Majalisar Dinkin Duniya ya tanada (UNSCR 1325).

Wacce ta cancanci a mika sunanta domin tantancewa;

 • Za a iya mika sunan mace ita kadai ko kuma kungiyar mata domin tantancewa.
 • An yarda ki ba da sunan ki da kan ki domin a tantance ki.
 • Duk wadda za a ba da sunan ta tilas ta kasance ‘yar kasar Afirka ce wadda kasar mamba ce a kungiyar Hada kan Afirka.
 • Komai shekarun mace za a iya ba da sunanta domin littafin da za a wallafa zai kunshi nasarorin da kuma gudumawa da mata, manya da kanana suke bayarwa ba tare da la’akari da shekarun suba.

SHARUDDAN BA DA SUNAN MACE

Wadanda za a ba da sunayensu tilas sukasance sun ba da muhimmiyar gudumawa a wadannan fannonin:

 • Sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya ko sun taimaka wa mata domin su taka muhimmiyar rawa domin samun zaman lafiya.
 • Sun ba da gudumawa mai yawa wajen hana ko dakile cin mutuncin mace ko hana yaduwar fyade da abin da ya shafi haka. Faxakar da mata alamomin da za su iya kai ga cin zarafinsu.
 • Ya kasance sun taimaka wajen cigaban mata da ‘ya’ya mata wajen samun kariya a zahiri da kuma inganta tunaninsu da cigaban tattalin arzikinsu da kare hakin mata da kuma sama musu kariya ta fannin shari’a.
 • Ya kasance mace ta taka muhimmiyar rawa wajen samun sauki ga ‘ya mace ta yin la’akari da abin da ya shafi Jinsi.
 • Ta kasance abar koyi wajen samun canji da nuna jajircewa da hazaka da kuma son nuna ita kanta abar koyi ce a cikin al’uma.
 • Ta kasance ta taka muhimmiyar rawa domin cigaban zaman lafiya da tsaro a matakin unguwa, kasa, shiyya, da ma Nahiya baki daya.

Ranar da za a rufe karbar sunaye;

Za a fara karbar sunayen da za ku turo nan take, kuma an kara wa’adin karbar sunaye zuwa ranar laraba 30 ga watan Satumba, 2021 da karfe 23:59 na GMT. Muna sa ran samun sunaye da dama, saboda haka wadanda sukayi nasara ne kawai za a tuntuba bayan tantancewa.

Ku lura da wadannan ka’idojin kafin ku tura sunan wacce za a tantance;

 • Kafin ka tura da sunan, tabbata ka/kin karanta sharuddan cancanta da kyau.
 • Tilas ka cika fam din da za ka/ki samu ta yanar gizo. Ki cika kuma ki aiko da shi ta imel (email).
 • Ba da sunan da bayanan su kasance babu kuskure a ciki.
 • Ya kunshi cikakken bayani da kuma inganci da cancantar wacce kika ba da sunanta.
 • Ba da sunayen daidaikun matan Afirka ko kungiyoyin mata wadanda suka yi aiki tukuru a matakin unguwanni shi aka fi so.
 • Ba da sunayen daidaikun mata ko kungiyoyin mata masu aiki a kauyuka tare da ‘yan gudun hijira. Mata nakasassu ko kuma mata wadanda wani bala’i ya kore su daga matsugunnansu, abin la’akari ne.
 • Yayin karbar sunayen wadanda za a tantance, za a yi la’akari da sassa na Nahiya saboda kowane sashen Nahiyar Afirka ya samu wakilci.
 • Za ku iya turo sunayen mata da tarihinsu a harsunan Ingilishi ko Larabci ko Potugis ko Faransanci.
 • Wadanda aka ba da sunayensu za su turo mana da hotunan fasfo wanda za a wallafa tare da cikakken tarinhinsu da lambar waya da adireshin email a cikin wannan ingantaccen Littafin da za a wallafa.

Domin shiga wannan takarar ko ba da sunan wacce ta cancanta, za ki iya samun fam din, a cika shi sannan a mika shi ta wannan adireshi; unoau-genderunit@un.org (kafar aikawa da email kafin a rufe karbar sunaye).

Kuna iya aika takardun shiga wannan gasar kai tsaye ta hanyar Google form.

Wadanda basu cancanci shiga ba:

Ba za a amince da takardun ba da suna ko shiga wannan gasar ba a bisa wadannan dalilai;

 • Ba da sunan mace ba tare da bayyana muhimmin gudumawar da ta bayar ba, sai kawai aka bayyana nasarorin da ta samu.
 • Rashin ba da cikakken bayanai tare da hujjoji wajen ba da sunan mace ko kungiyar mata.
 • An haramtawa ma’aikatan dake aiki tare da kowace Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ko kuma ta Kungiyar Hada kan Afirka, da kuma dukkan ma’aikatan wata Kungiya ta Shiyya ko kuma wata Cibiyar Tattalin Arziki da dai makamantansu.
 • Rashin ba da cikakken bayani game da mace da kuma yadda nasarorin da ta samu a rayuwasuka yi tasiri a wajen cigaban mata.

Shi wannan Littafi na yanar gizo, za a wallafa shi ne a harsunan Ingilishi da Faransanci.